(ABNA24.com) Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar da bayanin dangane da kamuwar wasu mutane 195 a kasar.
Rahoton na NCDC da ta fitar a daren jiya Talata, ya ce mutane 195 sun sake kamuwa da corona a cikin tsawon sa’oi 24, inda adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya yanzu ya kai 1,532.
Hukumar NCDC ta ce mutane 4 sun sake mutuwa a ranar jiya Talata sakamakon cutar a fadin Najeriya, abin da ya kai yawan wadanda annobar ta kashe zuwa 44 a halin yanzu.
A rahoton hukumar lafiya ta duniya, a dadin wadanda corona ta kashe a duniya ya zuwa yanzu ya kai mutane 218,000, yayin da wadanda suka kamu da cutar a duniya baki daya, adadin ya kai mutane 3,138,707, inda Amurka ita ce kasar da cutar tafi cin rayukan jama’a, ida ta kashe mutane 59,266, yayin da wadanda suka kamu da cutar a cikin kasar ta Amurka ya haura mutane 1,035,000.
/129
source : Hausa TV
Mittwoch
29 April 2020
06:22:02
1031249
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar da bayanin dangane da kamuwar wasu mutane 195 a kasar.