(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa, annobar corona za ta iya yin mummunan tasiri ta fuskar abinci a wasu daga cikin kasashen gabashin Afirka, da suka hada da Burundi, Jibouti, Habasha, Eritrea, Kenya, Rwanda, Somalia da kuma Uganda.
Bayanin ya ce a halin yanzu kimanin mutane miliyan 20 suke fuskantar matsala ta fuskar abinci a wadannan kasashe tun bayan bullar cutar ta Corona, sakamakon matsaloli daban-daban da suka faru sanadiyyar bullar cutar.
Bayanin ya ce wannan adadi zai iya karuwa zuwa mutane miliyan 34 har zuwa 43 daga watanni uku zuwa 6 masu zuwa, wanda hakan yasa hukumar take bukatar kudade kimanin dala miliyan 500 domin fuskantar wannan matsala a wadannan kasashe.
Hukumar ta bayyana cewa, baya ga matsalar corona, akwai wasu matsalolin da za su iya sanya wannan matsala ta kara kamari, da suka hada da fari da kuma farin dango.
/129
source : Hausa TV
Mittwoch
29 April 2020
06:22:02
1031247
Hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya FAO ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar matsalar corona ta haifar da matsalar abinci a wasu kasashe 9 na Afirka.