AhlolBayt News Agency (ABNA)

source : Hausa TV
Mittwoch

29 April 2020

06:22:02
1031246

Iran Ta Bukaci Hadin Kai Da Afirka Ta Kudu Don Tsamar Da Palasdinawa

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen Afirka ta kudu da kuma sauran kasashen duniya don kubutar da al’ummar Palasdinu daga zaluncin Amurka da kuma HKI. Har’ila yau da kuma samar da hanyar warware rikicin kasar Siriya ta hanyar tattaunawa.

(ABNA24.com) Tashar talabin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto shugaba Rouhani yana fadar haka a lokacin da yake zantawa da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a safiyar yau Talata ta wayar tarho.

Shugaban ya bukaci takwaransa na Afirka kan habaka dangantaka a harkokin kasuwanci da kuma na tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Har’ila yau Rouhani ya bukaci kasashen biyu su yi musayar bayanai kan dabarbarun yakar cutar Corona.

Daga karshe shugaban ya bukaci kasar Afirka ta Kadu a matsayin ta na mamba, na wucin gadi a kwamitin tsaro na Majalaisar Dinkin Duniya, ta yi kokarin kawo karshen son ran da Amurka take nuna wa a kwamitin tsaron. Musamman dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki ba tare da amincewar sauran yan kwamitin ba.

/129

Iran Ta Bukaci Hadin Kai Da Afirka Ta Kudu Don Tsamar Da Palasdinawa

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen Afirka ta kudu da kuma sauran kasashen duniya don kubutar da al’ummar Palasdinu daga zaluncin Amurka da kuma HKI. Har’ila yau da kuma samar da hanyar warware rikicin kasar Siriya ta hanyar tattaunawa.

Tashar talabin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto shugaba Rouhani yana fadar haka a lokacin da yake zantawa da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a safiyar yau Talata ta wayar tarho.