(ABNA24.com) Shugaban kasar Afghanistan ya gudanar da wata tattaunawa tare da Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif a daren jiya, kan batun dakatar da bude wuta a Afghanistan da kuma yin sulhu tsakanin bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar.
Ofishin shugaban kasar Afghanistan ya fitar da wata sanarwa a daren jiya cewa, shugaban kasar Ashraf Ghani, ya tattauna da Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi halin da ake cikia kasar ta Afghanistan.
Bayanin ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan batun sulhu tsakanin bangarorin siyasar Afghanistan, da kuma yin aiki tare domin dinke duk wata baraka wadda ka iya kawo cikas ga sha’anin mulki da siyasa a kasar.
Haka nan kuma da dakatar da bude wuta tare da komawa tattaunawa tare da kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar.
Baya ga haka kuma tattaunawar ta tabo batun dubban daruruwan ‘yan gudun hijira na kasar Afghanistan da suke a Iran, da kuma yadda kasashen biyu za su yi aiki wajen taimaka musu, musamman a cikin wannan yanayi na corona.
/129
source : Hausa TV
Mittwoch
29 April 2020
06:22:03
1031250
Zarif Da Ghani Sun Tattauna Kan Batun Dakatar Da Bude Wuta A Afghanistan
Shugaban kasar Afghanistan ya gudanar da wata tattaunawa tare da Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif a daren jiya, kan batun dakatar da bude wuta a Afghanistan da kuma yin sulhu tsakanin bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar.