AhlolBayt News Agency (ABNA)

source : Hausa TV
Mittwoch

29 April 2020

06:22:02
1031248

​Rasha: Ba Za Mu Goyi Bayan Haftar Kan Watsi Da Yarjejeniyar Sulhu A Libya Ba

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa, kasarsa ba ta goyon bayan matakin da janar Khalifa Haftar ya dauka na yin watsi da dukkanin yarjeniyoyin sulhu da gwamnatin Tripoli.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Inter-Fax ya bayar da rahoton cewa, a wani bayani da ya yi wa manema labarai jiya ta hanyar yanar gizo a birnin Moscow, Sergey Lavrov, ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa, Rasha ba ta goyon bayan matakin da janar Khalifa Haftar ya dauka na yin watsi da dukkanin yarjeniyoyin sulhu da aka cimmawa tare da bangarorin da suke takun saka a Libya.

Lavrov ya ce tun lokacin da aka gudanar da zaman tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin rikicin kasar Libya a birnin Berlin na kasar Jamus, Rasha ta bukaci da a tabbatar da amincewar dukkanin bangarorin rikicin a kan wannan yarjejeniya, tare da sanya hannu a kanta daga kowane bangare, domin rashin yin hakan zai iya kai wa ga rushewar yarjejeniya a gaba, amma wasu daga cikin mahalarta taron ba su amince da wannan shawara ta Rasha ba.

Ya kara da cewa, a halin yanzu Rasha tana ci gaba da tuntubar bangaren Haftar da gwamnatin Tripoli da kuma majalisar Tubruk, domin samun mafita, amma a cewarsa Rasha ba ta da wani iko na tilasta wani bangare daga cikinsu kan aiwatar da wani abu.

Lavrov ya ce Rasha ba za ta amince da matakin Haftar na yin watsi da duk wata yarjejeniyar sulhu ba, kamar yadda ba za ta amince da matakin shugaban gwamnatin Tripoli faez Siraj na kin amincewa ya gudanar da duk wata tattaunawa da Haftar ba.


/129